‘Sojojin Yemen sun kai hari kan jiragen ruwan Amurka take taimaka ma Isra’ila a yakin Gaza

Dakarun kasar Yemen sun ce sun gudanar da wasu sabbin hare-hare na yaki da Isra’ila da Amurka, inda suka auna wasu jiragen ruwa guda uku

Dakarun kasar Yemen sun ce sun gudanar da wasu sabbin hare-hare na yaki da Isra’ila da Amurka, inda suka auna wasu jiragen ruwa guda uku a cikin teku, ciki har da wani katafaren jirgin yaki na ruwa na Amurka mai ruguza makamai masu linzami da jirage marasa matuka.

Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Yahya Saree ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin Lahadi.

Ya ce an kaddamar da sabbin hare-haren ne a matsayin mayar da martani ga laifukan da Isra’ila ke aikatawa kan Falastinawea a zirin Gaza, da kuma ramuwar gayya kan hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen da Amurka da Birtaniya suka kai.

Saree ya kara da cewa, an kai harin farko ne kan wani jirgin ruwan yaki na Amurka da makamai masu linzami na ballistic, “a hari na biyu an auna jirgin Kyaftin Paris da wasu makamai masu linzami na ruwa da suka dace.”

Ya kara da cewa jirgin da aka kai wa hari yana kokarin karya matakin da sojojin Yaman suka shata ne na hana shiga tashar jiragen ruwa a yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta mamaye.

Dukkan hare-haren biyu an kai su ne a cikin Bahar Maliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments