Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ben Gurion Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Sojojin Yemen sun kai hari filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami guda biyu da kuma jirgin sama mara matuki ciki Sojojin Yemen

Sojojin Yemen sun kai hari filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami guda biyu da kuma jirgin sama mara matuki ciki

Sojojin Yemen sun sanar a yau Lahadi cewa: Sun kai hari kan filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makamai masu linzami guda biyu da kuma jirgin sama maras matuki ciki.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta bayyana cewa: Sojojin Yemen sun kai hari da makami mai linzami kan filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke Jaffa da makami mai linzami guda biyu, daya daga cikin makami mai linzami na Falastinu 2 da kuma makami mai linzamin Dhu al-Fiqar.

Sanarwar ta tabbatar da cewa, harin ya samu nasarar cimma burinsa, wanda ya sa miliyoyin ‘yan sahayoniya suka garzaya zuwa maboyar karkashin kasa, tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin na kusan sa’a guda.

Majiyar ta kara da cewa: Rundunar sojin sama ta kai wani samame a jiya da safe a kan tashar jirgin saman Ben Gurion da wani jirgin yaki maras matuki da ke Yaffa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments