Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ben Gurion Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Sojojin Yemen sun kai hare-hare kan filin jirgin saman Lod da ke Jaffa da aka mamaya da jiragen sama biyu marasa matuka ciki Sojojin Yemen

Sojojin Yemen sun kai hare-hare kan filin jirgin saman Lod da ke Jaffa da aka mamaya da jiragen sama biyu marasa matuka ciki

Sojojin Yemen sun sanar da kai wani farmakin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma nuna tsananin Rashin amincewa da kisan kiyashin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi kan ‘yan uwansu a zirin Gaza.

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau, inda ta ce farmakin da rundunar sojin saman Yemen ta kai da jiragen saman yaki marasa matuka ciki kirar Yaffa guda biyu, ya samu nasarar cimma burin da ake bukata.

Rundunar sojin ta yi nuni da cewa: A daidai lokacin da mahajjatan dakin Allah suke shirin tsayuwa a Arafat, suna tasbihi da gode wa Allah, ana ci gaba da zubar da jinin ‘yan uwansu a Gaza, ba tare da wani mataimaki ko mai ceto daga al’ummar musulmi ba, duk kuwa da irin karfin da za a iya kawo karshen wannan kisan kiyashi, wanda duniya ba ta taba ganin irinsa ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted