Zirga-zirgan jiragen sama ya tsaya cak a filin jirgin saman Sarki Fahad da ke Dammam a Saudiyya
Rundunar Sojin Yemen ta fadada ayyukanta masu tasiri sosai, bisa tsarin “ramuwar gayya ta hanyar kakaba takunkumin hana zirga-zirga,” ta hanyar tsawaita takunkumin hana zirga-zirgar jiragen sama da taka kakaba wa gwamnatin Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito cewa: Bayanan Flightradar24 sun nuna dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin saman Sarki Fahad da ke Dammam, gabashin Saudiyya, a ranar Asabar da yamma. Hukumar ba ta fayyace dalilan dakatarwar ba, amma masu fafutuka da kafofin watsa labarai na duniya sun ba da rahoton barazanar da aka yi wa filin jirgin.
Kafofin watsa labaran Saudiyya sun ambato wani mai magana da yawun Ma’aikatar Tsaro ta Saudiyya yana cewa: Tabbas an kai hari da makami mai linzami kan filin jirgin saman Dammam, yana mai fayyace cewa an kai harin ne kai tsaye a cikin filin jirgin.
A cewar wasu bayanai, waɗannan ci gaban sun nuna faɗaɗa ayyukan sojojin Yemen a cikin yankin Saudiyya, da nufin faɗaɗa iyakokin hare-hare a filayen jirgin sama da kuma ƙara tsaurara killace jiragen sama don ɗaukar fansa kan killacewar da Saudiyya ta yi wa Yemen.