Sojojin Yemen Da Hadin Gwiwar ‘Yan Gwagwarmayar Iraki Sun Kai Hare-Hare Kan H.K.Isra’ila

Sojojin Yemen da hadin gwiwar ‘yan gwagwarmayar Iraki sun kai hare-hare guda biyu kan jiragen ruwa biyar da suke jigilar kaya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila

Sojojin Yemen da hadin gwiwar ‘yan gwagwarmayar Iraki sun kai hare-hare guda biyu kan jiragen ruwa biyar da suke jigilar kaya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila

Sojojin Yemen da hadin gwiwar ‘yan gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki sun gudanar da wasu hare-haren soji na hadin gwiwa guda biyu kan jiragen ruwa da suke jigilar kayayyaki zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila karkashin taken; Taimakon al’ummar Falasdinu da ake zalunta da kuma mayar da martani kan hare-haren zaluncin da ake kai wa kan ’yan uwansu da suke Zirin Gaza.

Rundunar sojin Yemen a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa: Harin farko an kai shi ne kan wasu jiragen ruwa guda hudu a tashar ruwan Haifa, kuma biyu daga cikinsu, jiragen ruwan dakon siminti ne, sauran biyun kuma manyan jiragen ruwa ne mallakin wasu kamfanoni da suke karya dokar hana shiga tashar jiragen ruwan Falasdinu da aka mamaye, kuma hare-haren an kai sune ta hanyar jirage sama marasa matuka ciki.

A daya bangaren harin kuma, an kai shi ne kan jirgin ruwan Shorthorn Express a cikin tekun Mediterrenean, a kan hanyarsa ta zuwa tashar jiragen ruwa ta Haifa, da wasu jirage marasa matuka ciki, sannan majiyar ta tabbatar da cewa: Hare-haren biyu sun yi nasarar cimma burinsu kamar yadda aka tsara.

Sojojin Yemen sun kuma tabbatar da cewa; Za su ci gaba da gudanar da ayyukan soji na hadin gwiwa tare da kungiyoyin ‘yan gwaghwarmayar Iraki domin jaddada goyon baya da tabbatar da nasara ga al’ummar Falastinu har sai an daina kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments