Sojojin Sahayoniyya Sun Aiwatar Da Kisan Gilla Har Sau Hudu A Cikin Sa’o’i 24 Da Suka Gabata A Gaza

Falasdinawa da dama ne suka yi shahada kuma wasu adadi mai yawa suka jikkata a wasu sabbin hare-haren kisan gilla guda 4 da gwamnatin Isra’ila

Falasdinawa da dama ne suka yi shahada kuma wasu adadi mai yawa suka jikkata a wasu sabbin hare-haren kisan gilla guda 4 da gwamnatin Isra’ila ta kai kan Zirin Gaza

A ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan al’ummar Falasdinu a Zirin Gaza, sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi luguden bama-bamai kan yankuna daban-daban na Zirin Gaza, inda suka yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa fiye da 110 tare da jikkata wasu da dama a cikin sa’o’i 24.

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana cewa: Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun aiwatar da kisan gilla mai tsanani guda hudu, inda suka janyo shahadan Falasdina sama da 70 a wasu hare-haren kisan kiyashi a Beit Lahiya kadai, yayin da suka kai farmakin kan matsugunan Falasdinawa da suke cike da fararen hula wadanda suka kora daga muhallinsu.

A daya daga cikin hare-haren, jirgin saman yakin sojojin mamaya ya kai farmaki kan wani gida mai hawa 5 da ke Beit Lahiya, inda ya kashe akalla mutane hamsin tare da raunata wasu masu yawa.

Majiyoyin yankin sun bayyana cewa: Gidan da aka kai harin na dauke da mutane sama da 70 da suka rasa matsugunansu, kuma ya ruguje benen da wadanda ke cikinsa gaba daya. Sannan kisan kiyashin sojojin mamayar ya kuma shafi sansanin ‘yan gudun hijiran Jabaliya da birnin Gaza da sansanin Nuseirat da Bureij da kuma birnin Rafah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments