Search
Close this search box.

Sojojin Najeriya Sun Hallaka Kasurgumin Dan Bindiga, Kachalla Damina Da Yaransa

Kasurgumin ɗan bindigar nan da ya addabi jihohin Sakkwato da Zamfara da kuma Katsina, Kachalla Damina, ya baƙunci lahira tare da wasu daga cikin manyan

Kasurgumin ɗan bindigar nan da ya addabi jihohin Sakkwato da Zamfara da kuma Katsina, Kachalla Damina, ya baƙunci lahira tare da wasu daga cikin manyan yaransa.

Wannan na zuwa ne biyo bayan artabun da sojojin Nijeriya suka yi da Kacalla tare da yaransa bayan samun wasu bayanan sirri.

Bayan samun bayanan ne rundunar sojin saman Nijeriya suka yi dirar mikiya a kan maharan yayin da suke yunƙurin zuwa ƙauyen Ƙwana da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu ta Jihar Zamfara a ranar Lahadi.

Dama ƙasurgumin ɗan bindigar na fama da munanan raunukan da ya samu yayin wata arangama da ya yi da rundunar Operation Hadarin Daji a yankin Ɗansadau, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikin yaransa.

Bayanan sirri sun bayyana wa Zagazola Makama cewa kimanin babura 58 ne ɗauke da ‘yan ta’addar yayin da suke yunƙurin kai hari suka sha luguden wuta, wanda ake kyautata zaton cewa waɗanda suka tsira ba za su wuce 11 ba.

A harin dai an hallaka sama da ‘yan ta’adda 50 tare da kuma ƙone baburansu, a yayin artabun da suka yi da sojin Nijeriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments