Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Kemenei ya bayyana damuwarsa ga al’ummar Iran bayan da jirgin helikwafta da ke dauke da shugaban kasar Ibrahim Raeisi ya bata a wani yanki mai tsaunuka da ke arewa maso yammacin kasar Iran.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa “Muna fatan Allah Madaukakin Sarki ya mayar da shugaban kasa da tawagarsa su dawo cikin al’umma.”
Jagoran ya bukaci dukkan al’ummar Iran da su yi addu’a ga shugaba Raeisi da sauran jami’an gwamnatinsa da ke cikin jirgin.
“Kada al’ummar Iran su kasance cikin damuwa, ba za a samu cikas ga ayyukan kasar ba,” in ji shi.
Kawo yanzu Ana ci gaba da gudanar da wani gagarumin aikin ceto domin gano inda lamarin ya faru.
Saidai tsananin gurbacewar yanayi na yankin na kawo cikas ga ayyukan ceto.
An aike da tawagogin ceto kimanin arba’in a yankin da yanzu tuni dare ya shiga.