Dakarun sojojin Nijeriya sun samu nasarar kashe kasurgumin ɗan fashin daji, Kachalla Halilu Sububu a safiyar Juma’a.
Kafin kisan nasa, Kachalla ya kasance ubangidan ɗaya daga cikin manyan ’yan ta’addan nan Bello Turji.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz ne ya bayyana haka a shafins na Facebook.
Sojojin dai sun samu nasarar kashe ƙasurgumin dan bindigar ne bayan dauki ba dadi tsakaninsu da ’yan bindiga a tsakanin kwanar Dogon Karfe zuwa Mayanki a ƙananan hukumomin Moriki da Anka da ke Zamfara.
Hadimin Shugaban kasar ya ce, “wannan wata karin nasara ce bayan kashe wasu jiga-jigan ɓarayin daji da aka yi a cikin shekara ɗaya da ta gabata.
“Wadanda aka samu aikawa lahira a cikin wannan lokaci sun haɗa da Kachalla Ali Ƙawaje (kasurgumin dan ta’adda da ya taba harbo jirgin soja a Kaduna), Damina (mutumin da ya addabi yankin Dansadau), Moɗi-Modi, Galeri (wanda ya sace ɗaliban Kaduna), Dangote, da sauransu.