Sojojin mamayar Isra’ila sun sanar da kaddamar da farmaki kan yankin kudancin Siriya
Sojojin mamayar Isra’ila sun sanar da cewa: Da sanyin safiyar yau Laraba, jiragen yakinsu suka kaddamar da farmaki kan wasu wuraren soji a kudancin Siriya, kuma sun dora alhakin halin da ake ciki a kan gwamnatin Ahmed al-Sharaa.
Rundunar sojin mamayar Isra’ila a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: A wani lokaci kadan da ya gabata, bayan kai hare-hare kan yankunan haramtacciyar kasar Isra’ila, jiragen saman yakin na haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wuraren makaman gwamnatin Siriya a kudancin kasar ta Siriya.
Ta kara da cewa: Halaltacciyar gwamnati ce ke da alhakin halin da ake ciki a kasar Siriya, kuma za ta ci gaba da daukar nauyinta muddin aka ci gaba da nuna kyama ga yahudawan sahayoniyya daga yankinta, sojojin za su kalubalanci duk wata barazana da ke da hadari ga haramtacciyar kasar Isra’ila.
Tashar yada labarai ta kasar Siriya ta tabbatar da cewa: Jiragen saman Isra’ila sun kaddamar da farmaki a Tal Shaar da ke yankin Quneitra da ke kusa da birnin Izra da ke tsakiyar yankin Dar’a da kuma yankunan Sa’sa’ da Kanaker da ke yankin birnin Damascus fadar mulkin kasar.