Search
Close this search box.

Sojojin Kasar Yemen Sun Kakkabo Jirgin Sama Wanda Ake Sarrafashi Daga Nesa Na Kasar Amurka A Lardin Sa’ada

Kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah Saree ya bada sanarwan cewa sojojin kasar sun sami nasarar kakkabo jirgin saman yakin Amurka samfurin MQ-9 wanda

Kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah Saree ya bada sanarwan cewa sojojin kasar sun sami nasarar kakkabo jirgin saman yakin Amurka samfurin MQ-9 wanda ake sarrafa shi daga nesa a kan lardin sa’ada na kasar a jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Yahyah Saree yana cewa, banda haka sojojin kasar sun cilla makamai masu linzami kan wani jirgin ruwan kasuwanci mai suna Groton  a Tekun Aden saboda ya sabawa dokar kasar ta Yemen wacce ta hana dukkan jiragen ruwa  masu zuwa HKI ko na HKI wucewa ta yankin.

Labarin ya kara da cewa sojojin yamen sun yi amfani da makami mai linzami kirar cikin gida a kakkabo jirgin saman kasar ta Amurka wato MQ-9 a yankin Saada.

Gwamnatin kasar Yemen dai ta sha alwashin hana jiragen ruwan HKI da wadanda suke zuwa kasar wucewa ta mashigar ruwa ta babul Mandib tun cikin watan Octoban shekarar da ta gabata, har zuwa lokacinda za’a kawo karshen yakin da HKI take yi a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments