Sojojin Isra’ila Sun Kai Hare-Hare Kusa Da Hubbaren Sayyidah Zainab {a.s} Kusa Da Birnin Damascus

Hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya sun kai kusa da yankin Sayyida Zainab da ke gefen birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya Jiragen saman

Hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya sun kai kusa da yankin Sayyida Zainab da ke gefen birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya

Jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan wasu rumbunan ajiya da suke kusa da yankin Sayyida Zainab (amincin Allah ya tabbata a gare ta) a gefen birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya, lamarin da ya yi sanadiyar tashin bama-bamai na kayayyakin ajiyar.

Har ila yau jiragen saman yakin na ‘yan mamaya sun kai samame a rumbun adana kayayyaki na Qaldoun da ke yankin Jairud a gefen birnin  Damascus.

Rahotonni sun bayyana cewa: A jiya Litinin ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai hare-hare mafiya muni kan kasar Siriya tun shekara ta 2012, inda suka yi sanadin mutuwa da jikkatar fararen hula akalla 36, ​​sakamakon fashewar wasu bama-bamai a ma’ajiyar makaman da aka kai wa hari, da kuma harba makamai masu linzami da ba a saba gani ba a yankin Tartous.

Haka nan hare-haren sun haifar da babbar barna ga gidajen jama’ar kasar tare da kona dukiyoyinsu a kauyen Bilka da gidajen da suke kan hanyar Dreikish-Tartus.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments