Sojojin Isra’ila Sun Kai Hare-Hare Kan Yankin Gaza A Matsayin Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta

Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hare-haren bama-bamai da dama a gabashin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila sun yi rusa bama-bamai kan gidaje da dama a

Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hare-haren bama-bamai da dama a gabashin Zirin Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila sun yi rusa bama-bamai kan gidaje da dama a gabashin Zirin Gaza da safiyar yau Talata, tare da harba manyan bindigogi a yankuna daban-daban, a matsayin ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta.

Cibiyar Bayanai ta Falasdinawa ta ruwaito cewa: Tun daga wayewar gari a yau Talata, sojojin mamayar Isra’ila sun rusa gidaje da gine-gine akalla guda huɗu a gabashin birnin Gaza, Al-Bureij, da Khan Younis, inda aka ji ƙarar fashewar abubuwa masu karfi .

Cibiyar ta ƙara da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun buɗe wuta, ba tare da wani dalili ba a yankuna da dama na gabas da arewacin Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted