Sojojin Isra’ila Sun Harbi Masu Zanga-zanga Akan Mamayar Da Ta Yi Wa Syria

Sojojin HKI sun sanar da cewa sun harbi wasu mutane dake Zanga-zanga a kauyen Maariyah dake kusa da tuddan Gulan kusa da inda aka tsayar

Sojojin HKI sun sanar da cewa sun harbi wasu mutane dake Zanga-zanga a kauyen Maariyah dake kusa da tuddan Gulan kusa da inda aka tsayar da wutar yakin 1974.

Masu Zanga-zangar dai suna son ganin sojojin Isra’ilan sun kawo karshen mamayar da su ka yi wa kasarsu ta Syria.

Mutanen sun ce sojojin Isra’ilan sun kafa wurin bincike a cikin wani sansanin sojan Syria, sannan kuma sun hana manoma zuwa gonakinsu.

Har ila yau masu Zanga-zangar sun yi kira ga MDD da ta shiga cikin lamarin ta tilasata wa Isra’ilan kawo karshen mamaye kasarsu da ta yi. Tun bayan faduwar gwmnatin Basshar Asad ne dai Isra’ilan take kai wa Syria hari ta sama da kuma yin kutse ta kasa. Sojojin HKI sun ce, tun a makon da ya shude sun lalata kaso 70-80% na makaman kasar Syria

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments