Sojojin Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Beit Lahiya

Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun gudanar da kisan kiyashi a yankin Beit Lahiya sakamakon hare-haren bama-bamai da suka yi lugudensu kan yankin A daidai

Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun gudanar da kisan kiyashi a yankin Beit Lahiya sakamakon hare-haren bama-bamai da suka yi lugudensu kan yankin

A daidai lokacin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suke ci gaba da killace yankin arewacin Zirin Gaza, sun dauki matakin kai hare-hare kan mai uwa da wabi a yankin Beit Lahiya, inda suka aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula sama da 100 baya ga jikkata wasu na daban. Sannan wasu da dama sun bace.

Rahotonni sun bayyana cewa: A yammacin jiya Asabar sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun gudanar da wani mummunan kisan kiyashi ta hanyar jefa bama-bamai kan gidajen fararen hula da suke daura da Masallacin Al-Qassam da ke yankin Beit Lahiya a shiyar arewacin Zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin shahadar mutane akalla 73, a wani adadin farko da ofishin yada labaran gwamnatin Falasdinawa a yankin na Gaza ya sanar.

Baya ga wasu da dama da suka jikkata da kuma wadanda suka bace kuma yawancinsu yara da mata, kamar yadda ofishin ya sanar, rahoton yana nuni da cewa, wannan sabon kisan gilla ya zo ne tare da kawar da harkar kiwon lafiya a yankin Arewa wanda a halin yanzu yana dauke da kusan mutane 400,000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments