Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla 37 a safiyar yau a wasu hare-hare ta sama da suka kai kan masu gadi da ke rakiyar motocin agaji da kuma gidajen da suka kasance mafakar ‘yan gudun hijira a yankin Gaza da yaki ya daidaita.
Wata majiyar lafiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Falasdinawa 15 ne suka mutu sannan wasu 30 suka jikkata a wasu hare-hare biyu da Isra’ila ta kai kan masu gadi da ke rakiyar motocin agaji a yankunan yammacin Rafah da Khan Younis da ke kudancin Gaza.
A tsakiyar Gaza, an kashe karin Falasdinawa 15 a wani hari ta sama da Isra’ila ta kai kan wani gida da ke mafakar ‘yan kabilar Habbash a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, kamar yadda wata majiyar lafiya ta shaida wa Anadolu.
Wata majiyar lafiya ta kuma shaida wa Anadolu cewa Falasdinawa 7 ne suka mutu tare da jikkata wasu da suka hada da kananan yara a wani harin da Isra’ila ta kai kan wani gini a birnin Gaza.
Yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra’ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana 433 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,805 tare da jikkata mutum fiye da 106,257.