Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira

Rahotanni da suka fito daga yankin falasdinu sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun kai hari a sansanin yan gudun hijira dake gabar yammacin kogin

Rahotanni da suka fito daga yankin falasdinu sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun kai hari a sansanin yan gudun hijira dake gabar yammacin kogin Jodan kuma sun kashe wasu matasa guda biyu,da suka hada da jadalla jihar jumaa dan shekara 15 dake sansanin yan gudun hijira na fara’a a yammacin  garin Tubas.

Hukumar bada agaji ta yankin falasdinu ta bayyana cewa jami’anta sun kula da wasu mutane biyu da aka jikkata wato wani yaro dan shekara 16 da haihuwa da ya samu rauni a kugunsa, da kuma wani dan shekara 18  da shi ma ya ji rauni a lokacin da suke dauki ba dadi da sojojin Isra’aila a sansanin na fara’a, sai dai an hana ma’aikatansu zuwa daukar mutum na 3 da aka jikkata.

A wani labari na daban kuma sojojin isra’ila sun kashe hassan shakasi a wani samame da suka kai a sansanin askar dake gabashin Nablus, haka zalika su ma wasu falasdinawa guda biyu sun jikkata bayan da sojojin isra’ila suka afka musu a cikin wata motar taxi a garin jenin. Hare haren da Hki ke kaiwa a yammacin kogin jodan da ta mamaye sun yi tsanani sosai tun daga watan oktoban shekara ta 2023 wanda yayi sanadiyar mutuwar falasdinawa sama da 1073 yayin da wasu da dama kuma suka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments