Sojojin HKI Sun Kai Hari  A Sansanin ‘Yan Hijirar Falasdinawa Na al-Mawasi, dake kudancin Gaza

Majiyar labarai daga Gaza ta ce sojojin mamayar HKI sun kai harin ne akan sansanin ‘yan hijirar Falasdinawa na al-Mawasi, wanda  yake a yankin kudancin

Majiyar labarai daga Gaza ta ce sojojin mamayar HKI sun kai harin ne akan sansanin ‘yan hijirar Falasdinawa na al-Mawasi, wanda  yake a yankin kudancin Gaza.

Har ila yau rahotannin sun ambaci cewa bayan wani hari da sojojin mamaya su ka kai a yankin Khan-Yunus, har yanzu da akwai gawawwakin shahidai a karkashin baraguzai, kuma ‘yan mamayar sun hana ayyukan agaji isa wurin domin fito da su, ayi musu sutura.

Wata cibiyar Falasdinawa mai kididdigar adadin shahidai, ta bayyana cewa; Daga ranar 7 ga watan Oktoba, zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun  haura 33,000. A cikin wannan adadin da akwai kananan yara 14, da 350, wato kaso 44% na jumillar dukkanin shahidai.

Bugu da kari kididdigar ta ambaci cewa da akwai wasu kananan yara da adadinsu ya kai  43,000 da sun rasa daya daga cikin iyayensu, ko kuma sun rasa su baki daya.

MDD ta fitar da wani bayani wanda yake tabbatar da cewa da akwai mutane 7000 da su ka bace wadanda ba a san inda suke ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments