Ma’aikatar yaki na HKI ta bada sanarwan cewa sojoji kimani 70,000 suka zama guragu, ko sun rasa gabbansu ko kuma suka sami tabin hankali tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata. Banda haka wasu 8,663 suna jinya a halin yanzu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto rahoton ma’aikatar yakin na cewa, kashe 35% suna fama da matsalar kwakwalwa tun farkon yakin, a yayinsa wasu kashi 21% an sun ji raunuka daban daban.
Ma’aikata ta kara da cewa tana saran adadin wadanda zasu ji rauni zuwa karshen wannan shekarar da muke ciki zai karu da mutum 20,000.
Rahoton ya akalla sojoji 1000 ne ake kawowa don jinya a asbitocin HKI a ko wani wata. Inda kasha 20% na fama da tabin hankali. Kari kan wasu 9539 da suke fama da matsalolin hankali.
Sannan a ranar 7 ga watan yunin da muke ciki ne wani sojan HKi ya kashe kansa bayan an aiko masa da sakon ya sake komawa fagen fama.
Duk tare da asarori masu yawan wanda sojojin HKI suka yi a yankin na Gaza, ko Tufanul aksa, gwamnatin Natanyahu ta dage kan ci gaba da yaki har sai ta cimma manufofinta a yakin. Wannan kuma duk tare da kudurin kwamitin tsaro na MDD wanda ya bukaci a tsaida wuta da gaggawa, da kuma hukuncin kotun kasa da kasa ta ICC wacce ita ma ta bukaci a tsaida yakin a kuma gudanar da binciken kan abinda ya faru a Rafah. Da kuma daukar matakan hana kisan kare dangi.