Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Suna Kara Killace Arewacin Gaza Domin Tsananta Masifar Yunwa  

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare a fadin Gaza tare da kara killace arewacin Gaza domin kara habakar masifar yunwa Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare a fadin Gaza tare da kara killace arewacin Gaza domin kara habakar masifar yunwa

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na ci gaba da aikata laifin kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 426 a jere, ta hanyar kai hare-hare ba kakkautawa ta sama da kuma harba makaman roka, a yayin da suke aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula, a daidai lokacin da wani mummunan hali na jin kai ke kara ta’azzara sakamakon killace yankin da aka yi, inda Falasdinawa da suka yi gudun hijira suka haura sama da kashi 95% na al’ummar yankin.

Majiyoyin yada labaran Falasdinu sun watsa rahoton cewa: Jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila da makaman atilare sun ci gaba da kai hare-hare da kazaman bama-bamai a yau Alhamis a sassa daban-daban na Zirin Gaza, inda suke tarwatsa gidaje, sansanin ‘yan gudun hijira da hana zirga-zirga a kan tituna, inda suka kashe Falasdinawa masu yawa tare da jikkata wasu.

Har ila yau sojojin mamayar sun ci gaba da kai samame kan manyan unguwanni a birnin Rafah, tun daga ranar 7 ga watan Mayun da ya gabata, da kuma wasu yankunan Gaza, baya ga kai hare-hare ta hanyar jiragen sama da harba manyan bindigogi da sukejanyo munanan kisan kiyashi da kuma jefa bama-bamai a gidajen Falasdinawa a sansanin Jabaliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments