Sakamakon sabbin kisan kiyashi da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a Zirin Gaza an ci gaba da samun shahidai da jikkatan Falasdinawa
Wasu Falasdinawa da dama ne suka yi shahada, yayin da wasu kuma suka jikkata, a safiyar yau Lahadi, sakamakon farmakin da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar a kan yankuna daban-daban na Zirin Gaza, yayin da farmaki kan yankin ya shiga rana ta 303 a jere.
Falasdinawa biyar ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon harin bam da aka kai kan tantunan ‘yan gudun hijira da ke kusa da Asibitin Shahidan Al-Aqsa da ke Deir Al-Balah a tsakiyar Zirin Gaza.
Majiyoyin cikin gida a Falasdinu sun ruwaito cewa: Jiragen saman yakin sojojin mamaya sun yi ruwan bama-bamai a kan tantunan ‘yan gudun hijira da suka rasa matsugunansu da ke kusa da asibitin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 5 tare da jikkata wasu fiye da 16, baya ga wata babbar gobara da ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijiran.
Wasu Falasdinawan guda uku kuma sun yi shahada, yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani harin bam da jirgin saman yakin sojojin mamaya ya kai kan wani gida na iyalan Al-Hasanat da ke sansanin Deir Al-Balah da ke yammacin birnin na Gaza.