Shuwagabannin Iran Da Turkiyya Sun Jaddada Bukatar Karfafa Dankon Zuminci A Tsakaninsu

Shugaban kasar Iran ya zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Turkiya a jiya Lahadi, inda bangarorin biyu suka tattauna batutuwan da suka shafi

Shugaban kasar Iran ya zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Turkiya a jiya Lahadi, inda bangarorin biyu suka tattauna batutuwan da suka shafi dangantaka tsakanin kasar biyu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi yana taya tokwaransa na kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan shiguwar watan ramadan ya kuma roki Allah ya kara zaman lafiya da arziki gareshi da kuma mutanen kasar Turkiya.

Har’ila yau shugaban ya bukaci kasashen biyu sun tabbatar da cewa an aiwatar da yarjeniyoyin da suka cimma tsakaninsu a baya. Ya kuma bukaci kasashen biyu sun kara kyautata dangantaka tsakaninsu ta tattalin arziki zamantakewa da kuma makamashi.

A nashi bangaren shugaban kasar Turkiyya ya taya shugaba Ra’isi murnar shigowar watan mai alfarma na Ramadan, da kuma fatan Allah Ta’ala zai karbi ayyukammu ya kuma sanyamu cikin wadanda zai yenta daga wuta a cikin wannan watan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments