A ranar nuna goyon baya ga alummar falasdinu shugaban kasar Pakistan Asif Ali zardari ya jinjinawa Alummar falasdinu game da juriya da tsayin Dakar da suka nuna, yace jarumtar da suka nuna ta bude sabon shafin tarihi, don haka gudanar da bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka yana da muhimmanci sosai.
Kasar Pakistan tana da tarihin nuna goyon bayan alummar falasdinu , inda suka nuna goyon bayan alummar falasdinu na hakkin fayyacewa kansu makoma, a kudurin Lahore na shekara ta 1940,don haka wannan kiran na zardari ya kara jaddada tsohon matsayin Pakistan da ya doru kan nuna goyon baya, kwatar yanci da daidaito da kuma adalci.
Kiran da zardari yayi na gudanar da bincike kan laifukan yakin Israila yana nuna irin yadda kasashen musulmi suka damu da rashin daukar matakin doka kan ayyukan da isra’ila ke yi .
Ana sa ran Pakistan za ta ci gaba da fafutukar ganin an baiwa falasdinawa goyon baya a mataki na kasa da kasa, tana bukatar ganin an dakatar da bude wuta ta dindindin yadda za’a isar da kayan agaji, da kuma amincewa da falasdinu a matsayin kasa, kuma Pakistan za ta ci gaba da karfafa sakonninta na diplomasiya tare da bayyana ayyukan isra’ila a matsayin wadanda suka keta doka.