Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari

Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa harin da Amurka da isra’ila suka kai kan tashohin nukiliyar ta a tsakiyar

Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa harin da Amurka da isra’ila suka kai kan tashohin nukiliyar ta a tsakiyar watan yuli ya nuna cewa Amurka da kawayenta ciki har da isra’ila suna harin naurorin kimiyya na jamhuriyar musulunci ta iran ne.

Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da gidan talbajin din Al-Masirah na kasar Yamen inda ya jaddada” cewa ba’a taba kai irin wannan harin ba kan nauraron kimiyyar kasar a cikin tarihi, don haka yanayi kai harin yana nuna cewa Amurka da kawayenta sun shiga wani sabon mataki mai hadari, na karuwar tashin hankali kan yakin da suke yi da kimiyyar kasar iran.

A ranar 13 ga watan juni ne isra’ila ta kaddama da yaki kan kasar iran inda ta kashe manyan kwamandodjin sojojinta da masana nukuliya da sauran fararen hula ,

 bayan fiye da mako daya kuma Amurka ta shi ga cikin yakin kai tsaye inda tayi ruwan bama -bamai kan tashohin nukiliyar iran wanda hakan keta hurumin majalisar dinkin duniya da kuma yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukuliya NPT ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments