Shugaban Najeriya Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Ilimi don tabbatar da cewa, daliban jami’a suna ci gaba da

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Ilimi don tabbatar da cewa, daliban jami’a suna ci gaba da karatunsu ba tare da wani cikas ba, yana mai cewa, Gwamnatin Tarayya tana yin duk abin da ya dace don hana Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) tsunduma wani yajin aiki a nan gaba. 

Da yake magana da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, a ranar Talata, Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya umarce shi da ya nemo mafita mai ɗorewa ga duk wata matsala da ka iya kawo cikas ga ayyukan ilimi a manyan makarantun kasar nan.

Kamar yadda na gaya muku, Shugaban Ƙasa ya umarce mu da cewa, ba ya son ASUU ta sake shiga wani yajin aiki, kuma muna yin duk abin da ya dace don tabbatar da cewa dalibanmu suna makaranta,” in ji Alausa. “Yajin aikin na kwanan nan da suka yi na kimanin kwanaki shida bai dace ba don muna kan magana da su.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments