Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar najeriya Bola Ahmad tunubu ya mika sunayen mutane 32 ciki har da tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mahamud yakubu da tsohon ministan sufurin jiragen sama femi kayode ga majalisar dokokin kasar domin a tantancesu kwanaki bayan tura sunayen mutane 3 a fara da su.
Mai magana da yawun shugaban kasar bayo Onanuga shi ne ya fitar da sanarwa, a cikin wasu wasiku ma banbanta da shugaban kasar ya turawa shugaban majalisa Godswill Akpabiyo ya bukaci majalisar ta amince da sunaye 15 a matsayin jakadun aiki da kuma wasu 17 da bana aiki ba,
Akwai mata guda 4 daga cikin sunayen a matsayin jakadu na aiki da kuma wasu guda 6 a matsayin jakadu ba na aiki ba,
Ana sa ran tura sabbin jakadun a kasashen da najeriya ke da kyakkyawar alaka da su kamar su china, indiya koriya ta kudu , kanada, meziko , hadadiyar daular larabawa, Qatar , Afrika ta kudu, kenya, da kuma kungiyar tarayyar afrika da hukumar UNESCO, kuma zaa sanar da kasar da zaa tura kowannesu da zarar an gama tantancesu.