Shugaban Ansarullah: Yayi Gargadi Daukar Matakin Soji Kan Kasancewar Isra’ila A Somaliland

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yamen ya bayyana cewa kasancewa Isra’ila a yankin Somaliland za su dauke shi a matsayin inda za’a kai harin soji,

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yamen ya bayyana cewa kasancewa Isra’ila a yankin Somaliland za su dauke shi a matsayin inda za’a kai harin soji, domin ya zama babbar barazana ne ga kasashen somaliya da yamen da ma tsaron yankin wanda ya zama wajibi ne a kalubalanceshi da gaske.

Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin Abdul malik Al-Huthi inda yayi tir da sanarwar da isra’Ila ta yin a amincewa da yankin Somaliland a hukumance a matsayin kasa mai cin gashin kanta,

Har ila yau yace kasancewa Isra’ila a yankin na Somaliland zai zama babbar barazana ce kai tsaye ga tsaron yankin musamman ma tekun bahar maliya da gabar tekun hanyar zirga zirgar jiragen ruwa.

Sanarwar amincewa da yankin na somali landa da isra’ila tayi ya fuskancin yin allah wadai daga kasar somaliya kungiyar tarayyar Afrika kungiyar kasashen larabawa da sauran bangarori dake da karfi a yankin kuma sun bayyana shi a matsayin keta hurumin kasar somaliya ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted