Shugaban kasar Ukrain Volodomyr Zelesky ya samu tarba mai kyau a kasar Burtaniya bayan ya isa birnin London a jiya Asabar kuma bayan cacan baki mai zafi da yayi da shugaban Amurka Donal Trump a fadar White House dangane da yakin Ukraine.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa shugaba Zeleski ya gana da firaiministan kasar Burtania Keir Starmer, wanda ya yaba masa kan yadda ya tsayawa kasarsa da kuma kasashen turai a gaban shugaban Amurka Donal Trump da mataimakinsa a ranar jumma’an da ta gabata.
Labarin ya kara da cewa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya zanta da shuwagabannin biyu, wato Trump da kuma Zeleski don kwantar da hankali.
A yau Lahadi ce za’a gudanar da taro na musamman kan abinda ya faru tsakanin Zelesky da Trump da kuma makoman kasar Ukraine a yakin da take fafatawa da Rasha tun shekaru 3 da suka gabata.
Sauran shuwagabannin kasashen Turai sun yabawa Zelesky da yadda ya tsayawa kasarsa da kasa kasashen turai a tattaunawarsa mai zafi da manya-manyan Jami’an gwamnatin Amurka.