Shugaban Kasar Saliyo Ya Bukaci A Karawa Nahiyar Afirka Matsayi A Kwamitin Tsaro

Shugaban kasar Saloyi, ta bakin jakadan kasar a kwamitin tsaro na MDD ya bukaci a karawa nahiyar Afirka kujeru a kwamitin, musamman kujerun Veto. Shafinn

Shugaban kasar Saloyi, ta bakin jakadan kasar a kwamitin tsaro na MDD ya bukaci a karawa nahiyar Afirka kujeru a kwamitin, musamman kujerun Veto.

Shafinn yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto shugaba Julius Maada Bio yana fadar haka a taron kwamitin a ranar litinin da ta gabata, kan cewa nahiyar Afirka tana bukatar Karin kujeru a kwamitin tsaro na majalisar sannan da kasashe masu hakkin Veto har akalla guda biyu.

Kasar saliyo ce take shugabancin kwamitin tsaro na MDD a wannan watan, don haka ne shugaba Bio ya yi amfani da damar don sake nanata bukatar kasashen nahiyar Afirka ta samun karfi a kwamitin tsaro na majalisar. Ya kuma kara da cewa lokaci yayi da za’a bawa nahiyar Afirka hakkin nata a kwamitin tsaro na MDD a matsayin majalisa mafi karfi a duniya.

A halin yanzu dai kasashen Amurka, Rasha, China, Burtaniya da kuma Faransa ne mambobi na din- din-din a kwamitin tsaro na majalisar, kuma su suke da kujerar Veto. Sannan akwai kujeru 10 a kwamitin, wadanda ake jujjuyasu a tsakanin kasashen duniya, kafin shekara 1965 kujerun 6 ne, sai aka kara zuwa 10.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments