Shugaban Kasar Rasha Ya Sanya Hannu Kan Yarjeniya Ta Musamman Na Aiki Tare Da Iran Na Lokaci Mai Tsawo

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu a yarjeniya ta musamman na aiki tare da JMI na lokaci mai tsawo. Tashar talabijin ta Presstv

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu a yarjeniya ta musamman na aiki tare da JMI na lokaci mai tsawo.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa shugaban Putin ya amince da yarjeniyar ne bayan da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta kammala tsara yadda aikin tare da kasar Iran na lokaci mai tsaro zai kasance.

Labarin ya kara da cewa a jiya Laraba ce aka gabatarwa shugaban takardun bukatar kuma ba tare da wani bata lokaci ba ya sanya masu hannu. Dokar amincewa da wannan aiki taren dai bai  bayyana lokaci kawo karshen yarjeniyar ba, amma ya tabbatar da cewa aiki tare zai dauki lokaci mai tsawo.

Har’ila yau Putin ya sanyawa wannan yarjeniyar hannu ne a dai dai lokacinda shugaban majalisar koli na harkokin tsaron Rasha Sergei Shoigu  ya  ke ziyarar aiki a nan Tehran inda ya gana da manya-manyan jami’an gwamnatin JMI daga ciki da da shugaban kasa Masuod Pezeskiyan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments