Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi amanna da kiyaye ‘yancin kan kasar Armeniya da kuma ci gaba da huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Pezeshkian ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: “A ganawar da na yi da fira ministan kasar Armeniya, ya jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi amanna da kiyaye ‘yancin kan kasar Armeniya da kuma ci gaba da huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu. Dole ne a magance damuwar Iran game da kasancewar sojojin kasashen waje a kusa da kan iyakarta ta bai daya.”