Shugaban Kasar Iran Ya Tattaunawa Da Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Duniya

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kasarsa tana sa ran samun zaman lafiya da tsaro, amma za ta mayar da martani ga duk wani mataki

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kasarsa tana sa ran samun zaman lafiya da tsaro, amma za ta mayar da martani ga duk wani mataki da ya shafi tsaronta

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: A yau duniya ta cimma matsaya kan cewa Iran na son zaman lafiya da tsaro a duniya. Yana mai cewa, abin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke nema a fannin fasahar nukiliya ya yi daidai da tsare-tsare da lasisin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya.

A yayin ganawarsa da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi da ke ziyarar aiki a kasar Iran, shugaba Pezeshkian ya tabo batun ayyukan nukiliyar Iran na zaman lafiya da matsayinta na haramcin kera makaman nukiliya. Ya ce kamar yadda suka sha shelantawa kuma a kan fatawar Jagoran juyin juya halin Musulunci, ba su da niyya kuma ba zasu taba kera makaman kare dangi ba, sannan ba za su taba barin wani ya canza musu wannan manufa ba.

Shugaba na kasar Iran ya ci gaba da cewa: Kamar yadda suka sha nuna kyakyawar aniyarsu a baya, suna jaddada shirinsu na bada hadin kai da gudanar da hadin gwiwa da kusantar hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, domin kawar da shakku da zargin da ake yi kan ayyukan nukiliyar Iran na zaman lafiya da lumana, duk da cewa a yau duniya ta kai ga wannan tabbaci cewa Jamhuriyar Musulunci tana son wanzuwar zaman lafiya da tsaro a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments