Shugaban Kasar Iran Ya Mika Sakon Alhini Ga Lebanon Sanadiyyar Harin Ta’addancin HKI Ta Hanyar Wayoyin Sadanarwa

Shugaban kasar ta Iran Mas’ud Fizishkiyan ya kaddamar da ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar kasar Lebanon dangane da ta’addancin HKI ta amfani da hanyoyin sadarwa

Shugaban kasar ta Iran Mas’ud Fizishkiyan ya kaddamar da ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar kasar Lebanon dangane da ta’addancin HKI ta amfani da hanyoyin sadarwa da ta tarwatsa su daga nesa ta hanyar aikewa da sakwanni masu yawa da hakan ya yi sanadiyyar fashewarsu.

Shugaban na kasar ta Iran ya ce: “Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga mutanen Lebanon dangane da shahada da kuma jikkatar dubban mutanen Lebanon ta hanyar ta’addancin hanyoyin sadarwa, ba tare da tantance a tsakanin fararen hula da waninsu ba.”

Shugaban na kasar Iran ya yi addu’ar samun rahama ga wadanda su ka rasa rayukansu, tare kuma da yin addu’a ga Allah da ya dauki fansa akan HKI.

A shekaran jiya da kuma jiya HKI ta tarwatsa hanyoyin sadarwa da mutanen kasar Lebanon suke dauke da su, ta hanyar aikewa da sakwanni masu yawa.

Ministan yakin HKI Yoav Gallant ya bayyana cewa, abinda su ka yi, yana a matsayin bude sabon shafin yaki ne, da hakan yake a matsayin yin furuci da hannu wajen kai harin.

Kafafen watsa labarun Amurka sun bayyana cewa, sojojin HKI da kungiyar leken asiri ta Mosad ne su ka shirya kai wadannan hare-haren.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments