Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Aniyar Gwamnatinsa Na Wanzar Da Zaman Lafiya

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta yin jayayya da kowa, kuma ba zata zama mai biyayya ga girman kai

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta yin jayayya da kowa, kuma ba zata zama mai biyayya ga girman kai ba

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ta kuduri aniyar fadada dangantakarta bisa mutunta juna, amma ba za ta taba mika wuya ga girman kai ba.

Wannan dai ya zo ne a lokacin da shugaba kasar Iran Pezeshkian ya karbi bakwancin tawagar wakilan kwamitin tsaron kasa da manufofin kasashen waje na majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, inda ya yi bayanin fuskar da gwamnatin ta Sanya a gaba da jawaban gwamnati ta goma sha hudu, yana mai la’akari da cewa sulhu tsakanin al’umma da hadin kai a fagen siyasar cikin gida yana matsayin shimfida ce ga samun nasara a fagen siyasar harkokin waje.

Pezeshkian ya jaddada imaninsa cewa: Karfafa kasa ya dogara ne kan zaman lafiya da kuma cimma manufa daya da harshe guda wajen samun  daidaito batutuwa.

SHugaban na Iran ya kara da cewa: Fadada hadin gwiwa da hulda da dukkan kasashen duniya bisa mutunta juna shi ne abin da gwamnati ta sha hudu ta sa a gaba a fannin manufofinta na ketare, yana mai cewa: Ya sha bayyana cewa, ba za yi jayayya ko fada da wata kasa ba, kuma cewa tushen aikinsu ya ginu ne a kan zaman lafiya da abokanta da fadada alaka a kan tubalin fahimtar juna da mutunta juna a tsakani amma babu shakka za su tashi tsaye wajen fuskanta da kalubalantar masu girman kai da dagawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments