Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Karfin Sojin Iran Da Hadin Kan Al’ummar Kasar Sune Dalilan Samun Nasararta A Yaki

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa; Karfin sojojin Iran da hadin kan al’ummar kasa sune manyan dalilan samun nasara Iran a yakin baya-bayan nan Shugaban

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa; Karfin sojojin Iran da hadin kan al’ummar kasa sune manyan dalilan samun nasara Iran a yakin baya-bayan nan

Shugaban kasar Iran Masoud Pazeshkian ya ce: Idan ba don hadin kan al’umma da goyon bayansu ba, tare da karfin soji da makamai masu linzami na sojojin da suka lalata martabar ‘yan sahayoniyya da ba a kai ga nasarar da aka samu ba.

Pezeshkian ya kai ziyarar aiki ne zuwa ma’aikatar mai a safiyar Lahadin nan, inda ya yaba da kokarin ma’aikatan ma’aikatar da kuma manajojin ma’aikatar wajen ci gaba da gudanar da hidima a lokacin da yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran hari, ya kuma ce: Iran ta yi nasara a bangaren al’umma, albarkacin fahimta da hikima a daidai lokacin da makiya suke da Shirin aiwatar da barna inda aka dakile mummunan makircinsu na ruguza kasar.

Ya kara da cewa: Babban muhimmin abin da ake bukata don samun nasarar duk wani shiri, ko tsari na daidaita samar da makamashi da amfani da shi, da kuma samar da sahihin bayanai, na zamani da cikakkun bayanai da kuma samar da wadannan bayanai, wajibi ne a karfafa sadarwa tsakanin bangarori daban-daban, bisa la’akari da muhimmancin daidaita bangaren makamashi.

Muhimmancin saka hannun jari a masana’antar mai da fadada tashoshin wutar lantarki mai amfani da hasken rana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments