Shugaban kasar ta Jamhuriyar musulunci ta Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda ya gabatar da ta’aziyyar shahadar babban magatakardar kungiyar Hizbullah, Sayyid Hassan Nasrallah ya ce, a wani karon wannan laifin da ‘yan sahayoniyar su ka tafka ya sake tabbatar da cewa; babu abinda ya shafe su da dokokin kasa da kasa.
Bugu da kari shugaban na kasar Iran ya karyata cewa Amurka da kasashen turai sun bukaci Iran kar ta mayar da martani akan kisan Isma’ila Haniyyah, saboda a tsagaita wutar yaki a Gaza. Har ila yau, shugaba Fizishkiyan ya ce,kyale ‘yan Sahayoniya idan sun tafka wani laifi yana nufin an ba su dama su sake aikata wani a gaba.