Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya aike da sakonsa ga duniya baki daya, sakon da jaridar Tehran Times ta kasar Iran ta wallafa, inda a ciki ya yi bitar ra’ayinsa da matsayinsa kan batutuwan kasa da kasa da dama.
Daga cikin sakon, shugaban na Iran ya jaddada wajabcin dakatar da kisan kiyashin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a Zirin Gaza da kuma kawo karshen mamayar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa yankunan Falasdinawa.
Dangane da alakar yankin kuwa, Masoud Pezeshkian ta jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta sanya batun karfafa dangantakarta da makwabtanta a kan muhimman batutuwa da ta sa a gaba, kuma za ta yi kokarin gina wani tubali mai karfi a yankin da nufin habaka ci gabansa da bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da dukkan kasashensa.