Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Cewa Kasarsa Bata Neman Yaki Sannan Bata Nemam Mallakar Makaman Nukliya.

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa juyin juya halin musulunci  a nan Iran ya zo ne da sakon zaman lafiya ga dukkan kasashen

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa juyin juya halin musulunci  a nan Iran ya zo ne da sakon zaman lafiya ga dukkan kasashen duniuya, don haka ne ta haramtawa kanta mallakan makaman nukliya wanda yake kissan kare dangi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Alhamis a taron da jakadun kasashen waje da manya-manya baki suka halatta a gidan shugaban kasa a nan Tehran. Sai dai shugaban ya kara da cewa kissan kananan yara baa bin amincewa ne a garemu,

Sannan ya ce JMI bata amince da samuwar yan ta’adda a ko ina ba, kuma kasar Iran tana daga cikin kasashe wadanda suka fi cutuwa da ayyukan ta’addanci a duniya.

Sannan daga karshen  shugaban ya kammala da cewa tsarin harkokin wajen kasar Iran ya tafi ne a kan abota zaman lafiya da kuma mu’amala da juna cikin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments