Shugaban Kasar Iraki Ya Bayyana JMI A Matsayin Kasa Mai Muhimmaci A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Shuagaban kasar Iraki Abdullateef Jamal Rasheed yace JMI kasa ce mai muhimmanci a yanking abas ta tsakiya. Kamfanin dillancin labaran Sahab ya nakalto IRNA yana

Shuagaban kasar Iraki Abdullateef Jamal Rasheed yace JMI kasa ce mai muhimmanci a yanking abas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran Sahab ya nakalto IRNA yana fadar haka a yau Jumma’a sannan ya kara da cewa dangantaka tsakanin kasar Iraki da JMI tana da kyau, kuma zata kara karfi fiye da na yanzun.

Kafin haka dai Fu’ad Hussain ministan harkokin wajen kasar Iraki wanda yake cikin tawagar firai ministan kasar Muhammad Shia Assudani zuwa nan Tehran , ya bayyana cewa dangantaka tsakanin kasashen biyu suna da muhimmanci sannan jami’an kasashen biyu suna iya kokarinsu don ganin an aiwatar da dukkan ayyukan da kasashen biyu suke yinsu tare. Ko kuma ko wace bangare tana nata aikin.

Ya ce, har’ila yau, jami’an gwamnatocin kasashen biyu sun aiki kan dukkanin yarjeniyoyin da kasashen biyu suka cimma a tskaninsu, don aiwatar da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments