Shugaban Kasar Amurka Ya Sanya Hannu A Dokar Yin Tir Ta Kotun ICC Saboda Sammacin Kama Natanyahu Da Tayi

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya rattaba hannu a kan doka wacce ta yi allawadai da kutun kasa da kasa ta ICC saboda laifin fidda

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya rattaba hannu a kan doka wacce ta yi allawadai da kutun kasa da kasa ta ICC saboda laifin fidda sammacin kama abokiyar Amurka firai ministan HKI da ta yi, sanadiyyar kissan kiyashin da ya yi a gaza.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump ya na fadar haka a lokacinda yake rattaba hannu a kan dokar tasa a jiya Alhamis.

Ya kuma kara da cewa kotun da ke birnin huqae ta wuce huruminta a lokacinda ta cutar kawar Amurka HKI tare da fidda sammacin kama shi.

A ranar tarlatan da ta gabata ce Benyamin Natanyahu ya tattauna da shugaban Trump wanda yayi masa alkawula da dama, daga cikin har da  kwace Gaza daga hannun Falasdinawa ya maida su kasar Masar ko kuma wani wuri. Sannan gyra Gaza ya mikashi  ga falasdinawa..

Dokar ta zargi kotun ICC da shiga cikin abinda bai shafeta ba, na kokarin gano take hakkin bil’adamann da Amurka ta yi a Afganistan ko kuma kisan kare dangin da HKI ta yi a Gaza.

Don haka shugaban ya dorawa jami’an hukumar ta ICC takunkuman tafiya zuwa Amurka, wanda ya hada da iyalansu da kuma duk wanda ya taimaka wajen fidda sammashin.

A cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 ne kotun ta fidda sammacin kama Natanyahu da Glant saboda laifukan yakin da suka aikata a gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments