Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Suna gudanar da kyakkyawar tattaunawa da Iran
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Amurka na tattaunawa da Iran sosai kan Shirin makamashin nukiliyarta.
Donald Trump ya fada a ranar Laraba cewa: “Ya damu da abin da ke faruwa a Ukraine, kuma bai sani ba ko Putin na son kawo karshen yakin,” a cewar gidan talabijin na Al Jazeera.
Dangane da tattaunawar da aka yi da Iran, Trump ya ce: “Suna tattaunawa mai kyau da Iran.”
Trump ya ce: Dole ne bangarorin Gaza su amince da takardar da Steve Witkoff wakilin Amurka na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya ya gabatar.