Shugaban Kasar Aljeriya Ya Ce; Ba Zai Kai Ziyara Zuwa Kasar Faransa ba

Shugaban kasar Aljeriya ya nisanta yiwuwar gudanar da ziyarar aiki zuwa kasar Faransa saboda sabanin ra’ayoyi da ke tsakaninsu Shugaban kasar Aljeriya Abdulmadjid Tebboune zai

Shugaban kasar Aljeriya ya nisanta yiwuwar gudanar da ziyarar aiki zuwa kasar Faransa saboda sabanin ra’ayoyi da ke tsakaninsu

Shugaban kasar Aljeriya Abdulmadjid Tebboune zai yi watsi da yiwuwar kai ziyara zuwa kasar Faransa saboda koma bayan da aka samu rashin jituwa tsakanin kasashen biyu a cikin ‘yan kwanakin nan, kuma ya jaddada cewa; Yarjejeniyar shekara ta 1968 ta zama maras amfani a wajen masu ra’ayin rikau na Faransa.

Da yake amsa tambaya game da yiwuwar ziyararsa zuwa Faransa, a wata hira da gidan talabijin: Tebboune ya ce; Ba zan je Canossa ba wato ba zai mika wuya gaturawan mulkin mallakaba.

An kara samun koma baya a alakar da ke tsakanin kasar Aljeriya da Faransa tun a karshen watan Yulin da ya gabata, da Faransa ta ce za ta goyi bayan shirin mallakar kasar Moroko ga yankin yammacin Sahara.

Bayyana wannan matsayi ya Sanya Aljeriya cikin gaggawa ta kira jakadanta a Faransa, tare da rage yawan wakilanta na diflomasiyya a kasar ta Faransa, sannan ta wakilta mukaddashin jakadanta da ci gaba da gudanar da ayyukan jakadan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments