Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, zai kai ziyara ta farko a Masar cikin shekaru 11.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce shugaba Pezeshkian zai ziyara kasar Masar domin halartar taron koli na kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashe takwas da ake kira D-8, ziyarar farko da wani shugaban kasar Iran ya kai cikin shekaru 11.
Shi ma ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai jagoranci wata tawaga zuwa birnin Alkahira na kasar Masar domin halartar taron majalisar ministocin harkokin wajen kasar karo na 21 na kungiyar ta D-8 yau Laraba.
Za’a gudanar da taron na D-8 karo na 11 a ranar Alhamis, tare da halartar shugabannin kasashen musulmi takwas da ke halartar taron.
A gefin taron Iran za ta tattauna kan harkokin shiyya-shiyya da na alaka tsakaninta da Masar, musamman halin da Falasdinu da Lebanon ke ciki.
Kungiyar D-8 hada kasashen Bangladesh, Masar, Indonesia, Iran, Malaysia, Najeriya, Pakistan, da Turkiyya.
Ziyarar Pezeshkian a Masar za ta kasance ta farko da wani shugaban kasar Iran zai kai tun shekara ta 2013 lokacin da tsohon shugaban kasar Mahmud Ahmadinejad ya halarci taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Alkahira inda ya gana da shugaban Masar na lokacin Mohammed Morsi.