Shugaban Iran ya isa Rasha domin rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya isa kasar Rasha a zango na biyu na ziyarar da ya kai kasar Tajikistan. A safiyar Juma’a ya bar

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya isa kasar Rasha a zango na biyu na ziyarar da ya kai kasar Tajikistan.

A safiyar Juma’a ya bar birnin Dushanbe na kasar Tajikistan, inda ya tattauna da takwaransa na Tajikistan Emomali Rahmon kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu, shiyya-shiyya da kasa da kasa, tare da sa ido kan rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi na hadin gwiwa a fannoni daban daban.

A ziyarar tasa a birnin Moscow, shugaban na Iran zai gana da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, inda za su tattauna kan ci gaba da fadada hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da suka hada da kasuwanci, zuba jari, sufuri, fasaha, da al’adu, da kuma  batutuwan kasa da kasa,” a cewar Kremlin.

Bayan shawarwarin, bangarorin biyu za su rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da Rasha.

Sabuwar yarjejeniyar ta shekaru 20 ta shafi tattalin arziki, sufuri, makamashi, kiwon lafiya, da kuma fannin noma, baya ga hadin gwiwa tsakanin Tehran da Moscow don tinkarar kalubale na bai daya, da rage illar bala’o’i, da yaki da manyan laifuffuka, da yaki da ta’addanci, da kuma saka hannun jari na hadin gwiwa. .

Iran da Rasha dukkansu suna fuskantar takunkumin da kasashen yamma suka kakaba musu, wanda hakan yasa suka kara zurfafa hadin gwiwa da ke tsakaninsu dukkanin bangarori .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments