Cibiyoyin da babban daraktan hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ( IAEA), ya ziyarta sun hada Fordow ( Shahid Ali Muhammad) da Natanz ( Shahid Ahmadi Roshan) a yau juma’a.
Daga cikin wadanda su ka yi wa Grossi rakiya, da akwai mataimakin shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Behriz Kamalvandi da kuma mataimakin ministan harkokin waje Kazim Gharibabadi.
Rafael Grossi ya ziyarci cibiyoyin ne bayan tattaunawar da ya yi da jami’an gwmanatin Iran da su ka hada da shugaban kasa Mas’ud Fizishkiyan da ministan harkokin waje Abbas Arakci.
Wannan ziyarar ta Grossi ta zo ne a daidai lokacin da ake tattaunawa a tsakanin hukumar makamashin Nukiliya ta Iran da ta kasa da kasa domin warware rashin fahimtar dake tsakani.
Jami’an gwamnatin Iran sun tabbatar wa da shugaban hukumar makamashin Nukiliyar na Iran cewa, shirinsu na zaman lafiya ne.