Shugaban Amurka Yayi Barazanar Kakaba Harajin Kashi 25% Ga Kasashen Da Ke Huldar Kasuwanci Da Iran

Rahotani su bayyana cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi barazanar kakaba harajin kashi 25% cikin dari kan duk wata kasa dake hulda kasuwanci da

Shugaba Trump da Netanyahu

Rahotani su bayyana cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi barazanar kakaba harajin kashi 25% cikin dari kan duk wata kasa dake hulda kasuwanci da Iran, bayan shirin da Washington ta jagoranta na haifar da matsin lambar tattalin arziki a cikin kasar iran yadda zai kai a canza gwamnati.

Trump yayi wannan sanarwar ce a shafinsa na Trust social platform yace harajin zai fara aiki ne a nan take, sai dai bai bayyana kasashen da abin zai shafa ba, ko kuma yadda zai sanya harajin, sai dai ana ganin china a matsayin wadda tafi fitowa fili a cikin wannan mataki idan aka yi la’akari da girman cinikayya da take yi da kasar iran na biliyoyin daloli.

Bayan wannan barazanar Washington da Tel aviv sun goyi bayan masu tada tarzoma a kasar iran abaya bayan nan,  inda suka fara lalata dukiyoyin jama’a da kashe mutane a lokacin zanga-zangar  har ma suna rarraba makamai tsakaninsu  kamar yadda jami’an leken asiri a kasar iran suka tabbatar. Sai dai tuni mahukumta a iran suka gargadi jama’a game da wannan makirci  kuma jami’an tsaron iran sun kama da yawa daga cikin jagororin tada tarzomar dake da alak da hukumomin leken asiri na kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted