Shugaban Amurka Ya Ce: Nan Kusa Kadan Za A Kulla Yarjejeniyar Jakadanci Tsakanin Saudiyya Da Isra’ila

Sabon shugaban kasar Amurka ya bayyana yiwuwar kulla alakar jakadanci tsakanin Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila nan kusa kadan Sabon shugaban Amurka Donald Trump ya

Sabon shugaban kasar Amurka ya bayyana yiwuwar kulla alakar jakadanci tsakanin Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila nan kusa kadan

Sabon shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana game da yiwuwar kulla alakar jakadanci tsakanin masarautar Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila “nan ba da jimawa ba” da kuma gudanar da wata ziyara zuwa Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na rangadinsa na farko zuwa kasashen waje.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Al-Quds Al-Arabi a rahotonta cewa, hakan ya zo ne a lokacin da Trump ya mayar da martani ga tambayoyin ‘yan jarida a lokacin da yake rattaba hannu kan wasu shawarwari a ofishinsa da ke fadar White House, a yammacin jiya Litinin, bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar Amurka.

Trump ya ce: “Yana tsammanin Saudiyya za ta shiga cikin yarjejeniyar Abraham (…) nan ba da jimawa ba, a cewar Tashar talabijin ta “CNN” ta Amurka.

A shiga tsakanin Amurka, kasashen Larabawa hudu, wato Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain, Sudan da Morocco, sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin kulla huldar diflomasiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila a shekara ta 2020, kuma ana kiransu da “Yarjejeniyar Ibraham.”

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments