Shugaba Pezeshkian Ya Ce Ba’a Bukatar Wani Daga Waje, Kasashen Yankin Asiya Ta Kudu Zasu Iya Tabbatar Da Tsaron Yankinsu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa samuwar sojojin kasashen waje a kasashen yankin baya taimakawa kasashen. Shugaban ya kara da cewa Iran tana

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa samuwar sojojin kasashen waje a kasashen yankin baya taimakawa kasashen. Shugaban ya kara da cewa Iran tana son ganin ko wace kasa a yankin tana da cikekken yenta.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Pezeshkian yana fadar haka a jiya Litinin a lokacinda yake ganawa da mataimakin firai ministan kasar Azarbaijan Shahin Mustafayev, wanda yake ziyarar aiki a nan birnin Tehran.

Shugaban ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta fadada dangantaka tsakanin dukkan kasashen musulmi musamman makobta.

Ya ce: bama bukatar gina tatanga a kan iyakokin kasashemmu don tabbatar da tsaro. Kasashen yankin su bude kan iyakokinsu don harkokinka suwanci da zirga zirgan mutane. Ya ce yana bukatar a shimfiya layin dogo da kuma babbar hanya ta motoci tsakanin Iran da Azarbaijan

A nashi bangaren mataimakin firai ministan kasar Azarbaijan yace kasarsa tana bukatar fadada dangantaka da kasar Iran a fagagen kasuwanci, tattalin arziki tsaro da sauransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments