Shugaba  Kasar Ghana Ya Fitar Da Sunayen  Wadanda Za Su Jagorancin Harkokin Tattalin Arzikin Kasar

Shugaban kasar ta Ghana John Dramani Mahama wanda bai dade da saba layar kama aiki ba, ya sanar da sunayen wadanda za su jagoranci harkokin

Shugaban kasar ta Ghana John Dramani Mahama wanda bai dade da saba layar kama aiki ba, ya sanar da sunayen wadanda za su jagoranci harkokin tattalin arzikin kasar da su ka hada da minstan kudi Cassiei Ato Forson, sai kuma John Abdullahi Jinapor wanda zai zama ministan makamashi.

Mukamin babban ministan shari’a kuma babban mai shigar da kara na kasa kuwa an bai wa Dominic Akuritinga Ayine.

Dama tun a lokacin da yake yakin neman zabe ne Mahama wanda ya taba yin shugabancin kasar daga 2012 zuwa 2017, ya yi alkawalin cewa ba zai bata lokaci ba daga rantsar da shi, zai nada ministocinsa.

Daga cikin muhimman abubuwan da ya rika yin yakin neman zabe akansu da akwai batun tattalin arziki da farfado da shi,haka nan kuma fada da cin hanci da rashawa.

Ministan makamashi na yanzu Jinapor, ya taba rike wannan mukamin a lokacin da  Mahma ya yi shugabanci a baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments