Shehu Sani: Kissan Kiyashin  Da HKI Take Aikatawa A Gaza Da Lebanon Ya Nuna Cewa Babu Amfanin MDD

Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya a gwamnatin da ta shude ya bayyana cewa kissan kiyashin da HKI take

Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya a gwamnatin da ta shude ya bayyana cewa kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza na kasar Falasdinu da kuma kasar Lebanon ya nuna cewa kasashen duniya sun gaza wajen kawo karshen kisan mutanen a wadannan kasashe wanda HKI.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sanata shehu yana fadar haka a wata hira ta musaman da ta hadasu a birnin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. Ya kuma kara da cewa babu amfanin MDD idan ba zata hana kissan kiyashi irin wannan a duniya ba.

Sani, wanda kuma ya kasance shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama ta ‘Civil Rights Congress of Nigeria (CRCN)’ ya ce abinda yake faruwa a gabas ta tsakiya a halin yanzu yafi karfin kare hakkin bi’adama sai dai ana maganar dan’adamtaka .

Don a karon farko an ga kasashe wadanda suke riya democradiyya da kuma kare hakkin bil’adama sune suke goyon bayan HKI a kissan kare dangin da take yi a kasashen Falasdinu da Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments